Harin bom a kasar Pakistan | Labarai | DW | 29.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bom a kasar Pakistan

An kai wani harin kunar bakin wake a kan rundunar wanzar da zaman lafiya a Peshawar na Kasar Pakistan inda a kalla mutane 10 suka kwanta dama.

Rahotani daga Peshawar na kasar Pakistan, sun tabbatar da a kalla mutane 10 ne suka kwanta dama yayinda kusan 15 ne suka jikata a wani harin kunar bakin waken da aka kaiwa jami'an tsaro da sanhin safiyar yau.
Masu aiko da rahotani sun ce wani mutun ne ya tada jigidar bama baman dake daure a jinkinsa a dai dai lokacin wucewar ayarin motocin rundunar hadin gwiwar wanzarda zaman lafiya ta yankin a kusa ga ofishin jakadancin Amurka.
Kodayake wani babban komandan na rundunar tsaron Abdul Majeed Marwat wanda ya tsira da ransa ya shaidawa manema labarai cewar shi ne aka nufa da wannan harin. Wannan lamarin dai na zuwa ne mako daya bayan komawar tsohon shugaban kasar Perverz Musharraf wanda 'yan taliban su ka yi barazanar hallakawa.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Halima Balaraba Abbas