Harin bindiga a kan wani minista Libiya | Labarai | DW | 29.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bindiga a kan wani minista Libiya

Ministan cikin gida kana kuma muƙadashin firaminista Seddik Abdelkarim ya ƙetare rijiya da baya, bayan wani harin bindiga da aka kai masa

Masu aiko da rahotannin sun ce wasu mutane ɗauke da makamai da ba a tantace su ba, sune suka buɗe masa wuta a sa'ilin da ministan yake cikin motarsa.

Ministan dai na kan hayarsa ta halartar taron majalisar dokoki na ƙasar a lokacin da lamarin ya auku. Kuma nan gaba aka shirya ministan zai yi wani taron manema labarai domin ƙara ba da haske a kan abin da ya wakana. Wannan hari dai na zuwa ne makonni uku bayan kashe minista masana'antu na ƙasar Hassan Al Droui a garin Syrte da ke a gabashin Libiya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Umaru Aliyu