1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya salwantar da rayuka a Mekele

Mouhamadou Awal Balarabe
September 14, 2022

Mutane 10 sun mutu sakamakon harin bam da aka kai ta sama a Mekele da ke yankin Tigray na Habasha, a daidai lokacin da 'yan aware suka bude kofar tsagaita bude wuta da kuma yin shawarwarin zaman lafiya da gwamnati.

https://p.dw.com/p/4Gpa4
 Äthiopien Luftangriff  in Mekele, Tigray
Hoto: Million Haileselassie/DW

Wani jami'in asibitin birnin Mekele ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa wasu jirage marasa matuka guda biyu ne suka afka wa wata unguwar masu hannun shuni, inda mutane gona suka rasa rayukansu yayin da wasu karin mutane uku suka ji munanan raunuka.

‘Yan aware TPLF na Tigray sun nunar da cewa wannan dai shi ne karo na biyu cikin kwanaki biyu da dakarun gwamnatin Habasha suka kai hare-haren da jiragen saman a Mekele . Sai dai ya zuwa yanzu gwamnatin Firaminista Abiy Ahmed ba ta mayar da martani kan wannan zargi ba.

Rikicin ya sake barkewar a yankin na Tigray tun a ranar 24 ga watan Agustan 2022, lamarin da ya wargaza yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma watanni biyar da suka gabata tsakanin Habasha da kawayenta a bangare guda da kuma kungiyar TPLF a daya bangaren.