Harin bam ya ruguza ofishin jakadancin Faransa a Libiya | Labarai | DW | 23.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya ruguza ofishin jakadancin Faransa a Libiya

Masu gadin ofishin jakadancin Faransa da ke Libiya sun sami rauni sakamakon bam daya tarwatse a ofishin.

People stand among debris outside the French embassy after the building was attacked, in Tripoli April 23, 2013. France's embassy in Libya was hit by what appeared to be a car bomb on Tuesday, injuring two guards in the first such attack in the capital Tripoli since the end of the 2011 war that ousted Muammar Gaddafi. Residents living near the embassy compound, in the capital's Hay Andalus area, said they heard two blasts early in the morning around 0700 a.m. (0500 GMT). REUTERS/Ismail Zitouny (LIBYA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)

Ofishin jakadancin Faransa a libiya wanda bam ya ragaza

Gwamnatin kasar Faransa ta yi Allah wadai da harin da aka kaddama akan ofishin jakadancinta da ke birnin Tripoli na kasar Libiya a wannan Talatar. A cikin wata sanarwar da ministan kula da harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya fitar, ya ce Faransa za ta hada gwiwa tare da hukumomin Libiya domin yuin dukkan mai yiwuwa wajen gano musabbabin harin, da kuma wadanda ke da hannu wajen kaddamar da shi.

Tunda farko dai, wani jami'in ofishin jakadancin na Faransa a birnin Tripoli, wanda ya bayyanawa kanfanin dillancin labarai na Reuters batun harin, ya ce suna zaton bam din an dasa shi ne a wata motar da ke kusa da ofishin jakadancin. Ya kuma kara da cewar tarwatsewar ta janyo ta'adi da dama, baya ga masu gadi biyun da suka sami raunin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman