Harin bam ya kashe mutane 90 a Afghanistan
July 15, 2014Talla
Harin ya auku ne a lardin Paktika da ke a gabashin ƙasar kusa da kan iyaka da Waziristan yayin da wasu da dama suka jikata. Mataimakin shugaban 'yan sanda na yanki ya ce tun da fari a sanar da su za a kai harin ya kuma ce suna ƙoƙarin tare motar ne a lokacin da ta yi bindiga.
Masu aiko da rahotannin sun ambato wani jami'in yankin na mai cewar addadin mutane da lamarin ya rutsa da su na iya ƙaruwa. kana a Kaboul babban birnin ƙasar wani harin da Ƙungiyar Taliban ta ɗauki alhakinsa ya yi sanadiyyar mutuwar wasu 'yan jarida guda biyu da ke aiki a fadar shugaban mai barin gado Hamid Karzai kana wasu biyar suka jikkata.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu