Harin bam ya kashe mutane 50 a masallaci | Labarai | DW | 20.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya kashe mutane 50 a masallaci

Akalla mutane 50 suka rasu a tagwayen harin kunar bakin wake a wani masallaci a birnin Kabul na Afghanistan

A kasar Afghanistan wani harin kunar bakin wake da aka kai wani masallacin 'yan Shi'a a yammacin Kabul a ranar Juma'ar nan ya kashe akalla mutane 50 tare da jikkata wasu da dama.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida ta kasar Manjo Janar Alimast Momand yace dan kunar bakin waken ya je masallacin ne a kasa, ya shiga masallacin na Imam Zaman a birnin Dashti Barch sannan ya tada nakiyar da yake dauke da ita.

A waje guda kuma rahotanni sun ce wani harin na daban ya hallaka mutane 20 a wani masallacin a tsakiyar birnin Kabul yayin da suke shirin sallar Juma'a.

A wannan shekarar dai an sami yawaitar hare hare akan mabiya Shi'a a kasar ta Afghanistan.