Harin bam ya kashe mutane 20 a jihar Borno | Labarai | DW | 01.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya kashe mutane 20 a jihar Borno

An tabbatar da cewar mutane 20 ne suka rasa rayukansu a wani harin bama-bamai da sojoji suka kai ta sararin samaniya a kauyen Dagu da ke karamar hukumar Askira-Uba.

Akalla mutane 20 ne aka tabbatar da cewa suka mutu a wani hari da sojoji suka kai ta sama da bama-bamai kan kauyen Dagu da ke karamar hukumar Askira Uba na jihar Borno.

Harin kamar yadda mazauna yankin suka ce ya halaka mutanen ne wadanda akasarin su tsofaffi da kuma mata sai kuma karin wasu da suka ji munanan raunuka.

Wasu ma da suke fama da raunukan na kwance a halin yanzu a asibitin garin Mubi da ke Adamawa mai makwabtaka da jihar Borno. Wani da ke kwance a asibitin ya shaida yadda abin ya faru.

Rundunar sojin Najeriya dai ba ta ce uffan kan wannan barnar da aka yi zargin su ne suka haddasa ba.

Ko a ranar Juma'a ma, sai da ayarin gwamnan Adamawa Murtala Nyako ya katse ziyarar jajen da ya kai wa al'umomin Madagali da Michika da suka fuskanci hare-haren ‘yan bindiga, sakamakon harba harsasai da soji suka yi a garin Shuwa yayin da ayarin ke kokarin barin wajen.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita : Zainab Mohammed Abubakar