Harin bam ya kashe dan jaridan AFP
April 30, 2018Talla
Babu tazara a tsakanin fashewar farko da ta biyu inji Dawood Amin, wani babban jami'in 'yan sandan birnin , ya kara da cewa Shah Marai dan jarida mai daukar hoto na kafar yada labaran Faransa AFP ya mutu ne a sanadiyar hari na biyun a yayin da ya ke tsakiyar aiki. An dai shirya kai harin ne kan ginin da ake da tarin ofisoshi na kasashen ketare da ke yankin a cewar jami'in. Mutane sama da ashirin ne suka sami rauni a sanadiyar harin da ake zargin mayakan Taliban da kai wa a safiyar wannan Litinin.