Harin bam a Kabul a masallaci | Labarai | DW | 15.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam a Kabul a masallaci

Ya zuwa yanzu dai ba a san adadin mutanen da suka mutu ba, Wannan hari na zuwa ne mako daya bayan hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane sama dari a makon jiya a birnin na Kabul.

Rahotannin da ke zuwa mana yanzu-yanzu nan na cewar ban ta fashe a cikin wani masallacin yan Shi'a a birnin Kabul na Afghanistan wanda ke cike makil da jama'a daf da lokacin da ake shirin yin sallah magaruba. Ya zuwa yanzu dai babu wasu karin  bayyanai da aka samu  dangane da harin da ake kyautata zaton cewar na ta'addanci ne.