1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta halaka jagoran Kungiyar al-Shabab

Ramatu Garba Baba
April 7, 2020

Hare-hare ta sama da rundunar sojin Amirka ta kai a Somaliya ne yayi sanadiyar mutuwar jagoran Kungiyar al-Shabab Yusuf Jiis da wasu kusoshin kungiyar biyu.

https://p.dw.com/p/3abjS
Somalia Al-Shabaab Kämpfer
Hoto: picture alliance/AP Photo/F. A. Warsameh

Babban jami'in rundunar sojin Amirka a Afirka Stephen Townsend,  ya ce, wasu jerin hare-hare biyu da suka kai ta sama ya kashe babban kwamandan kungiyar al-Shabab a Somaliya. Yusuf Jiis da wasu kusoshin kungiyar biyu ne suka rasa rayukansu a farmakin na ranar biyu ga wannan watan na Afrilu inji Janar Townsend.

Amirka ta kwatanta Jiis da ta dadde tana nema ruwa a jallo, da mutum mara imani kuma azzalumi da ke da hannu a kisan fararen hula. Hakazalika ta ce yana adawa da gwamnatin kasar ta hanyar kai hare-hare kan jami'anta da gine-ginenta.

Duk da jan aikin yakar annobar Coronavirus da ke gaban gwamnatin Amirkan, ta ce ba zata sassauta matakinta na yakar Al-shabab ba. Kungiyar dai, na da alaka da kungiyar al-Qaeda, ta kuma kwashi shekaru tana kai hare-hare a Somaliya inda ta take da karfin iko da kasashen da ke makwabtaka da ita.