Harin al-Shabaab a Somaliya | Labarai | DW | 22.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin al-Shabaab a Somaliya

Kungiyar 'yan ta'addan al-Shabaab da ta addabi kasar Somaliya, ta yi ikirarin cewa ita ce ta hallaka wani jami'in leken asirin kasar Abdiweli Ibrahim Mohammed.

Mayakan kungiyar al-Shabaab a Somaliya

Mayakan kungiyar al-Shabaab a Somaliya

Mai tsaron lafiyar Mohammed ne dai ya harbe shi har lahira a garin Jowhar na kasar ta Somaliya. Abdiweli Ibrahim Mohammed dai ya kware matuka a harkar tsaro musamman fannin leken asiri, wanda da taimakon bayanan sirrin da ya ke ba wa jami'an tsaron kasar ta Somaliya ne ma, suka samu nasara a kan 'yan ta'addan na Al-Shabaab a kwanakin baya. Kungiyar ta Al-Shabaab na iko da yankuna masu tarin yawa a Somaliya, kuma ma ta na kiran kanta da kungiyar Al-Qa'ida reshen Gabashin Afirka. A kalla dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar hadin kan Afirka AU 22,000 ne, ke taimakawa gwamnatin kasar Somaliya a yakin da take da kungiyar ta Al-Shabaab.