Harin ƙunar bakin wake a Somaliya | Labarai | DW | 27.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ƙunar bakin wake a Somaliya

A Somliya ƙungiyar al-Shebab da ke da alaƙa da Al-Qaeda ta ƙaddamar da wani mummunan harin ƙunar baƙin wake a wani Otel a Mogadishu babban birnin ƙasar.

Wani babban jami'in ɗan sandan ƙasar Ahmed Abdi Fatah ya shaida wa kamfanin dillancin labaran ƙasar Faransa na AFP cewa tun da fari 'yan ta'addan sun tayar da bama-bamai a wajen Otel din na Maka al Mukarama kafin daga bisani su buɗe wuta a kan mai uwa da wabi. Ya ƙara da cewar kawo yanzu ba su da cikakken bayani kan addadin mutane da suka rasa rayukansu yayin wannan hari sai dai ya tabbatar da cewa jami'an gwamnati da dama na daga cikin waɗanda suka samu raunuka.