Hari ya jikkata sojoji kiyaye zaman lafiya a Mali | Labarai | DW | 16.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya jikkata sojoji kiyaye zaman lafiya a Mali

Hari ya jikkata sojoji kiyaye zaman lafiya a Mali yayin da aka koma kan teburin sulhu

Rahotanni daga arewacin ƙasar mali sun nuna cewar kimanin sojojin kiyaye zaman lafiya bakwai na Majalisar Ɗinkin Duniya suka samu raunika, sakamakon wata fashewa. Wasu majioyin soji sun ce lamarin ya faru a wannan Lahadi da ta gabta.

A wani labarin wannan Litinin aka koma teburin sulhu tsakanin mahukuntan ƙasar ta Mali da 'yan awaren arewaci a ƙasar Aljeriya. Majalisar Ɗinmkin Duniya ke taimaka wa shirin samun zaman lafiya tsakanin gwamnatin da Abzinawa.