Hari ya hallaka ′yan sandan Colombiya shida | Labarai | DW | 30.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya hallaka 'yan sandan Colombiya shida

Wani harin da ake dangantawa da kungiyar 'yan tawaye, ya hallaka 'yan sandan Colombiya shida.

'Yan sandan Colombiya shida sun hallaka, cikin wani harin kwantan bauna da aka kai musu, wanda ake dangantawa da kungiyar FARC mai ra'ayin makisanci.

Majiyoyin 'yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Yanzu haka ana ci gaba da zaman sulhu tsakanin gwamnatin kasar ta Colombiya da kungiyar 'yan tawayen, amma shugaba Juan Manuel Santos, ya kawar da yuwuwar tsagaita lokacin tattaunawar, har sai an amincewa da cikekken shirin sulhu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu