Hari ya hallaka sojan Mali 15 | Siyasa | DW | 26.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hari ya hallaka sojan Mali 15

Sojojin sun hallaka ne a wani harin da 'yan ta'adda suka kai wa sansanin jami'an tsaron a garin Sokolo da ke tsakiyar kasar a cewar sojoji da mazauna yankin

Wata sanarwar da rundunar sojan kasar dama mazauna yankin da lamarin ya faru suka tabbatar da aukuwar lamarin. Sanarwar sojoji cewa ta yi, an hallaka sojojinsu biyar a wani bariki da ke garin Sekolo. Wani jami'in soja da bai so a fadi sunansa ba ya fadawa kamfanmin dillalcin labaran AFP cewa, 'yan ta'adda kan babura rataye da muggan makamai sun dira wa barikin sojojin ba zata, suka yi ta bude wuta. Wani jami'in bada agajin gaggawa da ya samu kutsawa cikin barikin sojan, ya ce wurin duk a rude yake, kana ya kara da cewa ya kirga gawakin sojoji 15. Kasar Mali dai na fama da ta'addanci wanda ke sanadiyar rayukan jama'a.