1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An kai hari Tahoua a Jamhuriyar Nijar

Issoufou Mamane SB
November 17, 2021

'Yan bindiga da ba a tantance ba sun halaka kimanin mutane 25 a yankin kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar kusa da iyaka da kasar Mali inda ake samun tashe-tashen hankula na tsageru masu dauke da makamai.

https://p.dw.com/p/436np
Symbolbild Burkina Faso  Mehr als 138 Tote bei Anschlag
Hoto: Michel Cattani/AFP

A Jamhuriyar Nijar, rahotanni daga yankin Tahoua na nuni da cewa mahara dauke da makamai a kan babura da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai wasu tagwayen hare-hare a garuruwan Tebaram da Bakorat da ke yankin. Maharan sun yi dauki ba dadi da matasa da ke kare garin Bakorat, inda aka kwashe tsawon lokaci ana artabu kafin jami'an tsaron kasar suka isa yankin tare da taimakawa wajen dakile harin.

Gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Nijar tana kara matakan neman magance matsalolin tsaron da kasar ta shiga, saboda tashe-tashen hankula galibi a kasashe makwabta.

Mutane da dama sun halaka a kasashen yankin Sahel na yammacin Afirka tun shekara ta 2017, sakamakon hare-haren da ke ta'azzara na 'yan bindiga da ake dangantawa da masu matsanancin ra'ayin addinin Islama.