Hari kan filin jirgin saman Tripoli | Labarai | DW | 24.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari kan filin jirgin saman Tripoli

Wani hari da aka kai filin jirgin saman Mitiga da ke gabashin birnin Tripoli na kasar Libya ya yi sanadiyyar yin ta'adi ga wasu sassan filin jirgin saman.

Wani jami'i da ke aiki a wajen ya shaidawa manema labarai cewar wani jirgin yaki ne ya harba wasu makamai masu linzami kan tituna da jirage kan bi su sauka ko kuma su tashi sai dai ba a kai ga tantance wanda ke da hannu wajen harin ba.

'Yan bindigar nan na kungiyar Fajr Libya da ke rikici da mahukuntan kasar ne dai ke rike da wannan filin jirgin saman kafin a kai masa hari kuma shi ne filin jirgin sama daya tilo da dama yake aiki a birnin.