Hari da wuka a kasar Birtaniya | Labarai | DW | 06.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari da wuka a kasar Birtaniya

Jami'an 'yan sandan Birtaniya sun ce harin da wani ya kai kan wasu mutane da wuka na ta'addanci ne.

'Yan sanda na gudanar da bincike a Birtaniya

'Yan sanda na gudanar da bincike a Birtaniya

Mutumin dai ya kai harin ne kan wasu mutane uku a wata tashar jiragen kasa ta karkashin kasa a gabashin London. Rahotanni sun nunar da cewa guda daga cikin mutanen da ya caka wukar ya samu munanan raunuka yayin da biyun suka samu kananan raunuka, kafin jami'an 'yan sanda su samu nasarar cafke shi mutumin tare da tsare shi. A farkon mako mai karewa ne dai Firaministan Birtaniya David Cameron ya gabatar da bukatar tura sojojin Birtaniya zuwa Siriya gaban majalisar dokokin kasar inda suka kada kuri'a kan batun.