Hari a wurin jana′iza ya hallaka mutane a Kabul | Labarai | DW | 03.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari a wurin jana'iza ya hallaka mutane a Kabul

Mutane da dama ake sa ran sun hallaka a birnin na Kabul na Afghanistan a lokacin jana'izar wani da ya rasu a artabu da 'yan sanda lokacin zanga-zanga ranar Juma'a.

Wasu rahotanni na cewar mutane 20 ne suka rasu a Afghanistan bayan da wasu jerin bama-bamai uku suka tashi a wannan rana ta Asabar kusa da masu jana'iza ta wani da ya rasa ransa bayan taho mu gama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga a ranar Juma'a. Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin jami'an tsaro  da ma wasu da suka sheda yadda klamarin ya faru.

Wani da ya ga yadda abun ya faru da bai so a bayyana sunanasa ya ce mutane 12 ne yayin da wata kafar yada labaran talabijin a kasar ta Afghanistan Tolo News kuma ke cewa mutane 18 ne suka rasu.