1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ashraf Ghani ya tsallake rijiya da baya

Abdullahi Tanko Bala
September 17, 2019

Shugaban Afghanistan Asharfa Ghani ya tsallake rijiya da baya yayin wani harin kunar bakin wake da ya hallaka mutane kimanin 30 harin da 'yan Taliban suka dauki alhaki kaiwa.

https://p.dw.com/p/3Pjkj
Afghanistan | Selbstmordanschlag in Kabul
Hoto: Reuters/O. Sobhani

Wani harin kunar bakin wake da yan Taliban suka kai ya hallaka akalla mutane 30 a Afghanistan a yau Talata, hari mafi muni da aka kai kusa da wani wurin taron gangami da shugaba Ashraf Ghani ya halarta. sai dai shugaban ya tsallake rijiya da baya ba tare da ko kwarzane ba. 


Harin dai ya zo kwanaki goma sha daya gabanin zaben shugaban kasa a Afghanistan wanda kwamandojin Taliban suka ci alwashin sai sun wargaza a a kuma daidai lokacin da ake tattaunawar zaman lafiya tsakanin kungiyar yan tawayen da kuma Amirka.


Shugaba Ashraf Ghani wanda ke neman wa'adi na biyu na shekaru biyar a zaben da za'a yi a ranar 28 ga watan wannan watan na Satumba na shirin gabatar da jawabi a taron gangamin lokacin da dan kunar bakin waken ya kai hari.