1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a masallaci a Afghanistan

Abdourahamane Hassane
March 25, 2018

'Yan sanda a Afghanistan sun ce mutum daya ya mutu kana wasu guda bakwai suka jikkata a wani harin kunar bakin wake da wani dan bindigar ya kai a a cikin wani masallacin 'yan Shi'a da ke a garin Herat a yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/2uwFw
Afghanistan Anschlag auf Moschee in Herat
Hoto: DW/S. Tanha

Kakakin 'yan sanda na yankin ya ce mahara guda biyu ne suka yi shigar burtu a cikin masallacin daya ko da ya ankara an ganoshi take yanke ya tarwatsa kansa da bam din da ke a jikinsa kafin daga bisani a bindige dayan har lahira. Wannan shi ne karo na uku da ake kai  a garin na Herat.