Hari a kasar Mali | Labarai | DW | 22.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari a kasar Mali

Ana tuhumar 'yan tawayen kasar da kai hari kan otel a Bamako babban birnin kasar an dai kai harin ne a sansanin da sojojin kungiyar Tarayyar Turai ke amfani da shi don bai wa jami'an tsaron Mali horo.

Wasu mutane hudu suka nemi kutsawa cikin harabar otel din, wanda sojojin kungiyar Tarayyar Turai ke amfani da shi a kokarinsu na baiwa jami'an tsaron Mali horo. Masu gadin kofar shigan sun harbi daya daga cikin wadanda suka kawo harin, yayinda uku suka arshe. Cheick Salah Diallo, mazauni a anguwar da aka kai harin ya bayyana cewa. "Ba wanda ke da tsaro, kowa bai tsira ba. Amma dole ne dai jami'an tsaro su karfafa matakai, shi ne kawai mafita cikin wannan tashin hankali da muke ciki" Rundunar sojan kasar Jamus da ke aikin bada horon, ta tabbatar da kai harin, amma kuma a wani sakon da taikawa manema labarai ta bayyanan cewa, babu daya daga cikin dakarun ta da aka same shi a harin. Yankin da aka kai harin dai yana kusa da otel din Radisson Blue, wanda mayakan Alka'ida suka kai wa hari a karshen bara, inda suka yi sanadiyar mutuwar mutane 20.