1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSabiya

Wani ya kai hari a kan dan sanda a Sabiya

June 29, 2024

Wani mutumin dauke da kwari da baka ya raunata dan sandan kasar Sabiya da ke gadin ofishin jakadancin Isra'ila a birnin Belgrade.

https://p.dw.com/p/4hfqZ
Hoto: Marko Drobnjakovic/AP Photo/picture alliance

Dan sandan dai ya maida martani ta hanyar harbin maharin, ukumomin dukka kasashen biyu sun nuna cewa akwai alamar harin na ta'addanci ne. Ministan Ma'aikatar cikin gida na kasar Ivica Dacic a wata sanarwa ya ce  sai da maharin ya harba wa dan sandan wani abu tun da farko kuma abun ya daki wuyan jami'in.Ya kara da cewa dan sandan ya harbe maharin a kokarinsa na kare kai kuma raunuka da ya samu ne suka haddasa mutuwarsa.