1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 2, 2018

Kimanin mutane 16 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu sakamakon wasu jerin hare-hare da aka kai a coci da masallaci da kuma wasu asibitoci a Bangui baban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/2x2VJ
Zentralafrika Anschläge auf Kirche und Moschee
Jerin hare-hare a BanguiHoto: Reuters

Kafar yada labarai ta Vatican da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar ta ruwaito cewa, harin da aka kai a wata cocin mabiya darikar katolika mai suna Church of Fatima an kai shi ne da gurneti kana harin na masallaci da asibitoci aka kai shi da abubuwa masu fashewa. Rahotanni sun nunar da cewa mutane 100 ne suka jikkata sakamakon wannan hari. Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai na zaman guda daga kasashen Afirka da ke fama da tashe-tashen hankula da ke da nasaba da siyasa da addini da kuma kabilanci.