Hare-haren kunar bakin wake a Afghanistan | Labarai | DW | 11.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren kunar bakin wake a Afghanistan

Wasu jerin hare-hare da aka kai a wasu garuruwa guda uku na Afghanistan sun yi sanadiyyar mutuwar mutane guda 50 kana wau 80 suka jikkata.

Hare-haren wadanda wasu 'yan kunar bakin waken suka kai a birnin Kabul da da Helmand da kuma kudancin Kandahar tuni da Kuniyar Taliban ta dauki alhakin kai su.Masu aiko da rahotannin  sun ce addadin wadanda suka mutu yana iya karuwa saboda da yawa daga cikin wadanda aka kai a asibiti wadanda suka jikkatan suna cikin wani mawuyacin hali.