Hare haren jiragen saman Siriya
January 21, 2013Wata kungiyar kare haki bil adama ta kasar Siriya,ta babayana cewar a halin da ake ciki a garuruwan da suka hada da Erbine,Hamourie,Beit Saham,Mleha da ma Damscus na ci-gaba da fuskantar hare haren jiragen yakin dakarun gwamnatin Siriya. A yankunan Daraya garin da ke rike ga hannun 'yan tawayen,bayanaai sun yi nuni da mutuwar mutzane da dama ciki kwa har da yara kankana. A Damascus kwa,sakamakon hare haren,an samu daukewar wutar lantarki a duk fadin birnin,yayain da a na shi bangare,ministan harakokin wajen kasar ya sake jadda bukatar kawo karshen zubar da jini a kasar to amman sa fa kasashen wajen sun dfaiana tallafawa wadanda yxa danganta da 'yan ta'adda,ya kuma ce rikici a shirye gwamnatin ta ke ta zauna teburin sulhu da 'yan Siriya maza da mata masu korafi musamman wadanda basu dau makamakamai ba domin bullo da dabarun kawo karshen rikicin.