Hare-haren bama-bamai a Iraki | Labarai | DW | 13.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren bama-bamai a Iraki

Mutane 38 suka rasa rayukansu a garin Kirkuk da ke a yankin arewacin ƙasar inda lamarin ya auku.

Masu aiko da rahotannin sun ce wani ɗan ƙunar baƙin wake ne ɗauke da jigidar bama-bamai, ya kutsa kai a cikin wani gidan cin abinci a lokacin da jama'a ke yin buɗe baki inda ya tayar da bam ɗin.

Majiyoyin kiwon lafiya sun ce mutane da dama sun samu raunika kuma suka ce galibi waɗanda lamarin ya rutsa da su matasa ne. Kawo yanzu mutane kusan 300 suka mutu a cikin hare-haren tun daga farkon wannan wata da ya kama a ƙasar ta Iraki. Yawan tashe-tashen hankula da ake samu na saka fargaba a zukatun jama'ar dangane da ɓarkewar wani sabon faɗan tsakanin yan Shi'a da ke riƙe da mulki da kuma tsiraru 'yan Sunni.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh