Hare haren bama bamai a Birnin Kano na tarrayar Najeriya | Labarai | DW | 18.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare haren bama bamai a Birnin Kano na tarrayar Najeriya

Hukumar 'yan sanda ta JTF ta ce ta kama wasu mutane guda biyu,waɗanda ake zargi da dasa bam ɗin a kusa da fadar sarki Kanon mai martaba Alhaji Ado Bayero.

Da misalin ƙarfe Tara na daren jiya ne aka ji ƙarar wani abu da ake kyautata zaton cewar bam ne, wanda faruwarsa ta ƙara jefa al'ummar birnin Kano cikin ruɗani.

Musamman dangane da yadda a yan kwanakin baya baya nan aka ɗan samu sauƙin kai hare haren. Jama'a dai na kallon harin tamkar wanda ke da nasaba da ƙoƙarin da ake yi na zaman neman sulhu da nufin kawo ƙarshen tashin tashinar da ake fama da ita, ta rikicin kungiyar Boko Haram. Shaidu sun bayyana cewar bam ɗin ya fashe ne a daf da kofar fatalwa da ke jikin gidan sarkin kusa da harabar babban masallacin juma'a na jihar Kano daf da masarautar. Wasu mutane ne dai cikin babur mai kafa uku da ake kira da sunan a daidaita sahu suka dasa bam ɗin, sai dai kawo yanzu ba a san addadin wadanda suka mutu ba.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu