Hare-haren bam a jihar Yobe Najeriya | Labarai | DW | 18.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren bam a jihar Yobe Najeriya

Jami'an tsaro a birnin Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe da ke a yanki arewa maso gabashin Najeriya sun ce mutane da dama suka mutu a hare-haren da aka kai a wani gidan kallon wasan ƙwallon ƙafa.

Harin ya faru ne daf da lokacin da aka fara karawa tsakanin Brazil da Mexiko a ci gaba da gasar wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya da ake yi a ƙasar ta Brazil. kafofin yaɗa labarai na jihar sun ce wanda ya kai hari ya ajiye ƙushin bama-bamai a tsakiyar jama'ar da suka taru suna kallon wasannin.

Babban kwamishinan 'yan sanda na jihar Sanusi Rufai ya shaidawa manema labarai cewar yazuwa yanzu ba su da alƙalluma na addadin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Daman tun gabanin wasannin kwallon kafar na duniya hukumomin jihohin da dama na arewacin Najeriyar suka haramta wa jama'a yin kallon a irin waɗannan cibiyoyin saboda barazanar da Ƙungiyar Boko Haram ta yi na kai hare-hare

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu