Hare-haren bam a Biu da Jos | Labarai | DW | 26.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren bam a Biu da Jos

Wasu bama-bamai da suka tashi a garin Biu na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya da Jos a jihar Filato a tsakiyar kasar sun hallaka mutane da dama da jikkata wasu.

A kalla mutane 18 aka bada labarin rasuwarsu yayin da wasu 6 kuma suka jikata sanadiyyar tashin wani bam a garin Biu da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Wakilinmu na Gombe Amin Sulaiman Muhammad ya rawaito cewar lamarin ya faru ne da misalin karfe 3 na rana daidai lokacin da wasu mutane biyu suka nemi kutsawa cikin tashar mota da ake kira Tashar Gandu a Biu din inda nan take bam din da ke jikin daya ya tashi, yayin da aka cafke ragowar gudan kafin ya tada nasa bam din.

Can a birnin Jos na jihar Filato ma an samu tashin wasu bama-bamai har guda biyu. Wani da ya shaida lamarin ya gayawa wakilinmu Abdullahi Maidawa Kurgwi cewar ya ga gawawaki kan titi jim kadan bayan tashin bama-baman daura da wata tashar mota.

Ya zuwa yanzu dai jami'an tsaro sun toshe hanyoyin zuwa titin Bauchi da ke Jos din inda wannan bama-baman biyu suka tashi kuma ba su yi karin haske kan yawan wanda suka rasu din ba.