Hare-haren ƙunar baƙin wake a Iraki | Labarai | DW | 28.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren ƙunar baƙin wake a Iraki

Mutane 25 suka rasa rayukansu a cikin wasu jerin hare-hare da aka kai a wasu garuruwa daban-daban na ƙasar Iraki.

Majiyoyin kiwon lafiya da na tsaron sun ce hare-haren na ƙunar baƙin wake da aka kai a bisa kasuwanni da wuraren tsayuwar motocin bus,har ma da motocin da ke yi wa gawa rakiya, sun rutsa da farar hula da kuma jami'an tsaro. A kudancin Bagadaza motocin da dama ne bama-bamai suka tashi da su inda suka kashe mutane shida kana wasu goma suka samu raunika. Haka ma lamarin ya wakana a birninTikrit.

Tun farkon wannan shekara mutane dubu shida ne suka rasa rayukansu a cikin tashe-tashen hankula na Iraki galibi na addini da ƙabilanci.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe