Hare-haren ƙunar baƙin wake a Iraki | Labarai | DW | 17.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren ƙunar baƙin wake a Iraki

Mutane a aƙalla guda 32 aka kashe a jerin hare-haren da aka kai a yankuna daba-daban na ƙasar yayin da wasu da dama suka jikkata.

Majiyoyin kiwon lafiya sun ce motoci guda bakwai da bama -bama suka fashe a cikinsu a anguwannin daban-daban na birnin Bagadaza sun kashe mutane 24 yayin da wasu ɗari suka sami raunika.

A can yankin arewacin ƙasar kusa da garin Mossul an ba da rahoton harbe wasu 'yan sanda guda biyar har lahira,yayin da a Falluja da ke a yankin yammaci Bagadaza wasu mutane ɗauke da makamai suka kai hari a kan wani ofishin 'yan sanda inda suka tayar da abubuwa masu fashewa. To sai 'yan sandar sun ce dukkanin maharan guda huɗu sun mutu bayan da suka tayar da jikkidar bama-baman da ke a jikinsu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman