Hare haren ƙunar baƙi wake a Irak | Labarai | DW | 03.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare haren ƙunar baƙi wake a Irak

An sami asarar' rayukan jama'a da dama a sakamakon harin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kai a wani ofishin yan sanda

A wounded person is carried by soldiers at the site of a suicide bomb attack in Kirkuk, 250 km (155 miles) north of Baghdad, February 3,2013. A suicide bomber driving a car and gunmen disguised in police uniforms killed at least 33 people in the Iraqi city Kirkuk on Sunday when they tried to storm the police headquarters. REUTERS/Ako Rasheed (IRAQ - Tags: CIVIL UNREST)

hlag

An ba da rahoton cewar mutane a ƙalla guda 33 ne suka kwanta dama a harin wanda aka kai a garin Kirkuk da ke a yankin arewacin ƙasar Irak yayin da wasu guda 90 suka jikata.

Shaidu sun ce wani ɗan ƙunar baƙin wake ne, ya tayar da bam a sa'ilin da mutane ke fita zuwa wurin inda bam ɗin ta rusa wani ɓangare na wani ginin gwamnati. Majiyoyin likitoci sun ce daga cikin waɗanda suka mutu 12 ma'aikata ne a ginin ofishin gwamnatin da ya faɗi. Shi ma dai wanda ya kai harin da ke tare da rakiyar wasu maharan guda biyu ya mutu a cikin harin.Yazuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.


Mawallafi : Abdourahamne Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas