Hare-hare na ta′addanci a Kabul | Labarai | DW | 01.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare na ta'addanci a Kabul

Mutane kusan guda goma suka mutu a sakamakon wani harin ƙunar baƙin wake da wani dan bindigar ya kai a birnin Kabul na Afganistan.

Masu aiko da rahotonnin sun ce mutumin ya tayar da bam ɗin da ke a jikinsa a sa'ilin da ya isa a wajen wani taron jama'ar da suka ja dogon layi a bakin wani oifishin 'yan sanda da ke yammacin birnin

Tuni da Ƙungiyar Taliban ta yi iƙirarin ɗaukar alhakin kai harin.Kuma Yanzu haka ministan cikin gida na Jamus Thomas de Maiziere na yin ziyara a birnin na Kabul.Inda zai tattauna da hukumomin ƙasar a kan buƙatar dakatar da yawan kwararan 'yan gudn hijira daga Afganistan ɗin zuwa Jamus.