Hare-hare akan sansanonin ′yan tawayen Mali | Labarai | DW | 13.01.2013
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare akan sansanonin 'yan tawayen Mali

Faransa ta bayyana rusa sansanonin baiwa 'yan tawayen Mali horo, yayin da 'yan kasar ta Mali ke nuna goyon baya ga matakin soji akan 'yan tawayen.

Kasar Faransa ta bayyana cewar a wannan Lahadin ne dakarunta suka kaddamar da hare hare akan sansanonin 'yan tawayen Mali da ke garin Gao a yankin arewacin kasar. Ma'aikatar kula da harkokin tsaron Faransa ta ce jiragen saman yaki hudu ne suka yi ta jefa bama-bamai a garin, a kokarin da suke yi na dakile 'yan tawayen. Sanarwar da ma'aikatar tsaron Faransar ta fitar, ta ce hare haren sun la'la'ta sansanonin da 'yan tawayen ke yin anfani da su wajen bayar da horo ga mayakansu da wasu na'urori da kuma kayayyakin da suke yin anfani da su. Wannan dai shi ne yini na ukku - a jere da kasar Faransa ke bata-kashi da 'yan tawayen kasar Mali, wadanda ke da iko da yankin arewacin kasar tun kimanin watanni tara da suka gabata.

A halin da ake ciki kuma, 'yan Mali da dama ne suka yi tururuwa zuwa cibiyoyin daukar jini domin bayar da jinin na su a matsayin gudummowa ga fafutukar kwato yankin arewacin kasar daga hannun 'yan tawayen. Wasu daga cikin fararen hular da suka je cibiyoyin, sun bayyana cewar, tunda ba su da kudin da za su bayar a matsayin tallafi ga dakarun da ke fafutukar dakile mayakan Ansar Dine da ke da iko a yankin arewacin kasar, to hanya daya tilon da ta rage musu ita ce bayar da jininsu. A dai wannan Jumma'ar ce shugaban Mali ya bukaci 'yan kasar - mazansu da matansu dama kanfanonin da ke hada-hada a kasar, da su tallafawa kokarin kawo karshen ikon da 'yan tawaye ke da shi a wasu sassa na kasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal

 • Kwanan wata 13.01.2013
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17JHm
 • Kwanan wata 13.01.2013
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17JHm