Hare-hare a Kabul daf da bukukuwan Ashura | Labarai | DW | 11.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a Kabul daf da bukukuwan Ashura

An ba da rahoton cewar wasu mutanen dauke da makamai sun bude wuta da bindigogi ga wasu mabiya 'yan Shi'a a kusa da wani wurin ibada a birnin Kabul na Afghanistan.

Wani kakakin gwamnatin Afghanistan ya tabbar da cewar an kai hari a wurin ibadar jama'ar sai dai kuma bai bayyana ba addadin mutanen da suka mutu.Sallah Ashura wacce mabiya Shi'a ke yi a kowace shekara na yin tuni  da zagayowar ranar da Iman Hussein jikan manzon Allah,aminci Allah da tsira su tabbata a kansa ya rasu a hijira ta 680.