Hare-hare a Jihar Filato ta Najeriya | Labarai | DW | 07.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a Jihar Filato ta Najeriya

An kashe mutane huɗu, kana aka raunata wasu biyar a farmakin da wasu mutane ɗauke da makamai suka kai a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Wase ta jihar Filato.

Rahotanni sun ce maharan su kimanin mutum 30 suka kai harin a ƙauyen Lamba Gyambar da ke cikin ƙaramar hukumar ta Wase ɗauke da miyagun makamai, inda suka yi ta yin ɗauki ba daɗi tare da jami'an tsaro kafin daga bisani su yi galaba tare da ƙona gidaje da dama.

Wani da ke da zama a ƙauyen ya sheda wa wakilinmu na jihar Filato, Abdullahi Maidawa Kurgwi, halin da suke ciki bayan harin kan cewar an yi asara mai yawa. Kuma a halin da ake ciki wasu rahotannin na cewar mazauna ƙauyen na Lamba Gyambar, yanzu haka suna ficewa daga ƙauyen zuwa ƙauyuka mafi kusa saboda tashin hankalin.

Mawallafa : Abdullahi Maidawa Kurgwi / Abdourahamane Hassane
Edita :Mohammad Nasiru Awal