Hare-hare a garin Kumo na jihar Gombe | Labarai | DW | 26.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a garin Kumo na jihar Gombe

An ji karar harbe-harbe da fashewar abubuwa a Kumo da ke Gombe, a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

An kwashe daren jiya ana jin karar harbe-harbe da fashewar wasu abubuwa masu karfi da ake zaton bama-bamai ne, bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai garin Kumo mai nisan kilomita 50 daga Gombe fadar gwamnatin jihar Gombe dake Arewa maso gabashin Najeriya.Tun da misalin karfe 11 na daren jiyan ne dai mazauna garin Kumon suka fara jin karar harbe-harbe, tare da muryoyi dake yin kabbara. Wasu dake makobtaka da ofishin ‘yan sanda na garin suka ce an kai hari a ofishin ‘yan sanda.

Sai dai babu wani cikakken bayani kan wadanda wadannan hare-hare ya rutsa da su saboda cikin dare abin ya faru. Wannan dai shi ne karo na farko da aka kai irin wannan hari a yankin, wanda a baya ke karkashin dokar-ta-bacin da shugaba Jonathan na Najeriya ya ayyana a jihohin Borno da Yobe da Adamawa. Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da hukumomin suka bayar kan wadannan hare-hare inda kuma babu wata Kungiya da ta dauki alhakin kai hare-haren.

Mawallafi : Al-Amin Suleiman Muhammad
Edita : Saleh Umar Saleh