Haramcin takara ga magoya bayan Blaise Compaoré | Labarai | DW | 08.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haramcin takara ga magoya bayan Blaise Compaoré

Gwamnatin wucin gadi ta Burkina Faso ta ba da sanarwa cewar ta kawo sauye-sauye ga kundin tsarin mulki na ƙasar.

Burkina Faso ÜbergangsPräsident Michel Kafando

Michel Kafando shugaban gwamnatin wucin gadi na Burkina Faso

A kan waɗannan sauye-sauye gwamnatin ta haramta wa magoya bayan tsohon shugaban ƙasar wato Blaise Compoare tsayawa takara a zaɓuɓɓukan da za a gudanar a ƙasar.

Hakan kuwa ya biyo bayan da majalisar dokokin ƙasar ta kaɗa ƙuria'r amincewa da daftarin ƙudirin wanda gwamnatin ta gabatar da shi a gareta. A cikin watanni na gaba da ke tafe ne za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da na 'yan majalisu a Burkina Faso.