1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Harajin sigari na yi wa ‘yan siyasar Lesotho barazana

Zainab Mohammed Abubakar ZUD
April 1, 2022

Wasu daga cikin 'yan siyasar Lesotho dai na fargabar cewar idan aka kara farashin taba sigari, babu wanda zai jefa musu kuri'a a nan gaba.

https://p.dw.com/p/49M6i
rauchender Mann
Hoto: Colourbox

Jaridar Die Tageszeitung wadda ta yi sharhi kan gagarumar nasarar da sabuwar jam'iyyar adawar kasar Zimbabuwe ta yi a zaben cika gurbi na majalisar wakilai, ta ce nasarar hadakar jam'iyyun neman canji a zaben da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata, na nunar da cewar kasar ta sake fadawa cikin yanayi mawuyaci a siyasance.

 

Jaridar ta ce A bangaren jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar ta Emmerson Mnangagwa da kuma sabuwar jam'iyyar adawa ta CCC ta Nelson Chamisa, zaben cike gurbi na kujeru 28 daga cikin kujeru 210 na 'yan majalisar dokokin da aka gudanar, tamkar sharar fage ne ga zabuka masu muhimmanci da ke tafe a shekara ta 2023.

Simbabwe | Kundgebung der Opposition in Simbabwe
Hoto: Tsvangirayi Mukwazhi/AP/picture alliance

Jam'iyyar adawa ta CCC ta lashe kujeru 19 cikin 28, yayin da jam'iyyar ZANU-PF ta samu kujeru tara. Sai dai har yanzu jam'iyya mai mulki na ci gaba da rike rinjayenta a majalisar dokokin kasar baki daya. Don haka yanzu kowa na iya jin kamar wanda ya yi nasara. Sai dai Hausawa kan kance ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

 

"Annobar Afirka ta gaba" wannan shi ne taken labarin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi a kan yawaitar masu shan taba a nahiyar Afirka. Jaridar ta ci gaba da cewar, a yayin da yawan masu shan taba a duniya ke raguwa, a Afirka karuwa suke. Wannan garabasa ce ga masana'antun yin taba na kara yawan tabar da suke sarrafawa.

 

Mahooana Khati na zama muhimmin dan siyasar Lesotho da ke cikin fargabar yiwuwar sake zabensa. Tsawon yini dan majalisar da sauran takwarorinsa suka dauka suna muhawara kan kudirin da yake son kauce wa na sanya harajin taba. Lesotho ta kasance daya daga cikin kasashe a Afirka da ake sayar da sigari ba tare da harajinta, hakan ne ta sa tabar kan kasance da arha.

 

A yanzu haka dai farashin taba ya fi komai sauki musamman ma wadanda ake sayarwa ta bayan fage. Ba tare da tuntubar hukumomin lafiya ba, gwamnati ta kara harajin taba na kaso shida maimakon 30 daga cikin 100 na kudirin farko.

 

Dangane da haka ne kamfanonin taba sigari ke wa Afirka kallon, nahiyar da za su ci gagarumar moriya a yanzu da ma kuma nan gaba, har a kananan kasashe kamar Lesotho mai yawan al'umma miliyan biyu kacal. Hukumar kula da lafiya ta MDD ta ce, an samu raguwar masu shan taba a fadin duniya cikin shekaru 20 da suka gabata, inda a yanzu haka yawan masu shan taba ya tsaya a biliyan 1.3. Sai dai a Afirka an samu karuwar yawan masu shan taba daga miliyan 64 zuwa miliyan 73.

Lesotho Moeketsi Majoro wird als neuer Premierminister vereidigt
Hoto: Getty Images/AFP/M. Molise

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung sharhi ta wallafa mai taken "Muna dab da fadawa bala'i". Yankin gabashin Afirka na fama da fari mafi dadewa cikin shekaru da dama da suka gabata. Damina uku ke nan a jere ba a samu girbi mai kyau ba a yankin kahon Afirka. Mata da yara kanana kan  yi tafiyar kilomitoci masu yawa kafin su samu ruwa.

 

A kasashen Habasha da Somaliya da Kenya, wajen mutane miliyan 14 ne ba su da isasshen abinci, rabin wannan adadin kuwa yara kanana ne. Miliyoyin mutane na kaura saboda neman ruwa, kuma masana yanayi sun yi hasashen karin miliyoyin wasu nan ba da jimawa ba. Dabbobi na mutuwa, a yayin da albashin da mutane ke samu bai taka kara ya karya ba.