Har yanzu Mali na cikin rikici | Labarai | DW | 16.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu Mali na cikin rikici

Ƙasar Mali an samu asarar rayuka bayan harin da aka kai wa sojojin rundunar MINUSMA ta Majalisar Ɗinkin Duniya hari lafiya inda aƙalla mutane uku suka mutu kana wasu 16 suka jikkata.

Wani ɗan kunar bakin wake dai ya tarwaza kansa a sansanin sojojin Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya kashe fararen hula uku. Kana wasu kimanin 16 suka jikkata. Akasarin wadanda aka jikkatan ma'aikata masu aikin kiyaye zaman lafiya ne. An yi kiyasin jami'ai kimanin dubu 10000, ke a sansanin na MDD a Mali, inda suke aikin dawo da doka da oder a ƙasar, tun bayan da 'yan ta'addan Al-Qaida suka rikita ƙasar a shekra ta 2012.