Har yanzu ba ta sake zani ba a Mali | Labarai | DW | 08.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu ba ta sake zani ba a Mali

Ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya guda hudu 'yan kasashen ketare sun rasa rayukansu yayin wani hari a Mali.

Hari a wani Otel a Mali

Hari a wani Otel a Mali

Rahotanni sun nunar da cewa ma'aikatan na Majalisar Dinkin Duniya da kuma direbansu dan kasar Mali na daga cikin mutane 12 da suka rasa rayukansu yayin wani hari da aka kai a wani Otel a Malin. Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniyar a Mali MINUSMA ce ta tabbatar da hakan inda ta ce ma'aikatan na Majalisar Dinkin Duniya da suka rasa rayukan nasu sun hadar da 'yan kasar Ukraine biyu da dan kasar Nepal guda da kuma dan kasar Afirka ta Kudu guda. A wannan Asabar din dai an samu nasarar kawo karshen garkuwar da maharan suka yi da mutanen da ke cikin Otel din tun a ranar Jumma'ar da ta gabata.