Har yanzu ba a gano jirgin saman fasinjan Malaysia da ya fadi cikin teku ba | Labarai | DW | 10.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu ba a gano jirgin saman fasinjan Malaysia da ya fadi cikin teku ba

Baya ga neman wurin da jirgin ya fadi, ana kuma mayar da hankali kan wasu mutane biyu wadanda suka shiga jirgin da fasfunan kasashen Turai biyu da aka sata.

Har yanzu ba a yi nasarar gano jirgin saman fasinjan kasar Malaysia da ya fadi cikin teku kusa da kasa Vietman ba. Jiragen sama da na ruwa masu yawa ke aiki ba dare ba rana suna nema jirgin saman a wani babban yanki mai fadin murabba'in kilomita 100 tsakanin gabar tekun Malaysia da kuma Vietnam. Daraktan hukumar zirga-zirgar jiragen saman Malaysia Azharuddin Abdul Rahman ya fada a Kuala Lumpur babban birnin kasar cewa ana gudanar da binciken a dukkan bangarori, kasancewa ba a san ainihin abin da ya faru da jirgin ba, inda ya ce: "Firaminista yayi amfani da kalmar rashin tabbas. Mu din ma muna cikin rashin tabbas. Muna bukatar kwakkwarar shaida, muna bukatar ganin buraguzan jirgin kafin mu tabbatar da ainihin abin da ya faru a wannan rana."

Kawo yanzu dai ana magana game da hatsari ko kuma harin ta'addanci ka iya zama sanadiyar bacewar jirgin saman samfurin Boeing 777. Masu bincike sun mayar da hankali kan wasu mutane biyu wadanda suka shiga jirgin da fasfunan kasashen Turai biyu da aka sata.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh