1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sauran mutane sama da 40 da gini ya danne a Afirka ta Kudu

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 8, 2024

Jami'an agajin dai sun samu damar magana da mutane 11 da ke karkashin ginin, kuma suna amfani da karnuka masu sansano abubuwa, sannan akwai ma'aikatan lafiya jibge a wurin

https://p.dw.com/p/4fbxS
Hoto: Esa Alexander/REUTERS

Jami'an agaji a kasar Afirka ta Kudu na ci gaba da aikin ceto mutane sama da 40 da har yanzu ke karkashin baraguzan gini mai hawa 5 da ya rufta musu, a daidai lokacin da suke tsaka da aikin gina shi, inda ya zuwa yanzu suka samu nasarar kubutar da mutane 26.

Karin bayani:Tsohon shugaban Afirka ta Kudu ya tsallake rijiya da baya

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai ginin ya ruguje a yankin George da ke kusa da birnin Cape Town, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6, daga cikin ma'aikata 75 da ke tsaka da aiki a lokacin faruwar lamarin.

Karin bayani:WHO ta ce babu sauran gurbataccen maganin tari a Afirka

Jami'an agajin dai sun samu damar magana da mutane 11 da ke karkashin ginin, kuma suna amfani da karnuka masu sansano abubuwa, sannan akwai ma'aikatan lafiya jibge a wurin, don samar da duk wani taimakon gaggawa da ake bukata yayin aikin ceton.