Hankoron neman zaman lafiya | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 06.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Hankoron neman zaman lafiya

Shirin telebijin don neman fahimtar juna da zaman lafiya ta amfani da littattafai masu tsarki na addinan Kirista da Musulunci ba tare da daga murya ba.

A wannan makon ma jaridun na Jamus sun rubuta labarai da dama game da nahiyarmu ta Afirka, daga ciki har da neman zaman lafiya a arewacin Najeriya da aikin hakar zinari a Afirka ta Kudu.

A labarinta mai taken hankoron neman zaman lafiya jaridar Die Tageszeitung ta ce mace-mace da ayyukan tarzoma sun mamaye kanun labaru, to amma mabiya addinan Kirista da Musulunci a arewacin Najeriya na koyan darasi daga juna musamman don neman zaman lafiya.

"Tashar telebijin mai zaman kanta ta AIT mai shelkwata a Abuja tana watsa wani shiri mai taken Dandalin addini ko kuma "Interfaith Forum" sau biyu a mako da ke kokarin kawar da bambamci tsakanin Kirista da Musulmi. Kimanin mutane miliyan 50 ke kallon wannan shiri inda ake tattaunawa tsakanin Prista George Ehusani da kuma Imam Muhammad Nuruddeen Lemu. Wannan dandalin na amfani da ayoyi daga littattafai masu tsarki na addinan biyu ba tare da daga murya ba, inda suke kira ga samun fahimtar juna. Wannan salon na tattaunawa ko yin sulhu tsakanin addini wani abin yabawa ne musamman a arewacin Najeriya me fama da rikicin addini da na kabilanci, inda kuma ayyukan ta'addanci na kungiyar nan da ake wa lakabi da Boko Haram ya kara jefa yankin cikin mawuyacin hali na rashin tsaro."

Yajin aiki ya kawo cikas ga tattalin arziki

Wani sabon yajin aikin gama gari ya jefa gwamnatin Afirka ta Kudu karkashin jagorancin ANC cikin halin na tsaka mai wuya, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung sannan sai ci gaba kamar haka.

"Tattalin arzikin Afirka ta Kudu ya fuskanci koma baya sakamakon yajin aikin gama gari da ma'aikata a kamfanoni da dama ciki har na motoci da mahaka zinari ke yi. A ranar Talata ma'aikata hako zinari kimanin dubu 80 sun ajiye aikinsu suna masu neman karin albashi. Sai dai kamfanonin sun ce ba za su iya biya wa ma'aikatan bukatunsu ba, domin a cewarsu sun yi rauni sakamakon wasu yaje-yajen aikin da aka yi a wasu bangarorin hakan ma'adanan karkashin kasa. Ko da yake an cimma wani kwarkwaryan daidaito a ranar Laraba da rana amma har yanzu da sauran aiki a gaba. Ko da yake Afirka ta Kudu ke samar da kashi daya bisa uku na zinari a duniya, amma kamfanonin hakan wannan arziki sun yi rauni, kuma sai an yi hako mai zurfin gaske karkashin kasa kafin a cimma wani abin kirki, wanda haka ke kara yawan kudin da aka kashewa wajen tafiyar da aikin."

Yaki ya daidaita gabacin Kongo

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung labari ta buga a kan abin da ta kira nasarar da Majalisar Dinkin Duniya ta samu a Kongo-Kinshasa tana mai cewa sojojin duniya na amfani da sabon kudurin Kwamitin Sulhu suna fatattakar 'yan tawaye, sannan sai ta kara da cewa.

"Bayan shekaru masu yawa tana zura ido ba tare shiga yakin ba, yanzu kan Majalisar Dinkin Duniya tana fada gadan-gadan a gabacin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo. Kungiyoyin 'yan tawaye masu gaba da juna musamman kungiyar M23 sun daidaita yankin na gabacin Kongo. Ita kuma rundunar kiyaye zaman lafiya ta Monusco mai sojoji dubu 19, tana samun nasara tun bayan fadada aikinta a cikin makonnin da suka gabata. Sai dai masu sanya ido a kan abin da ka je ya komo ba su hango lokacin kawo karshen rikicin nan gaba kadan ba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe