Haniyeh yayi watsi da batun sauke gwamnatinsa | Labarai | DW | 20.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Haniyeh yayi watsi da batun sauke gwamnatinsa

Firaministan Palasdinwa Ismail Haniyeh yace zai turjewa duk wani yunkuri da shugaba Mahmud Abbas zaiyi na hambarar da gwamatinsa,yana mai gargadin cewa yin hakan ba zai kawo kaeshen zaman tashin hankali na yankin ba.

Haniyeh yace duk wata hukuma da Abbas zai nada ba zata samu amincewar majalisa ba wadda kungiyar Hamas take da rinjaye.

Abbas dai ya nuna alamun korar gwamnatin Hamas bayan kokarin kafa gwamnatin hadaka yaci tura,saboda kin sassautowar Hamas daga kan matsayinta game da Israila.

Haniyeh yace Abbas ba shi da iko karkashin doka,na kiran zabe ko kafa wata gwamnati ta wucin gadi.