1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hango mafiyata daga rikicin Mali

December 7, 2012

Ƙungiyoyin 'yan tawaye biyu da gwamnatin Mali sun amince da shirin tsagaita wuta a wani mataki na samar da kyakkyawan yanayin ci gaba da tattaunawa.

https://p.dw.com/p/16yMK
Hoto: AFP/Getty Images

Tattaunawa da 'yan tawayen Mali, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai mayar da hankali da shirin tsagaita wuta da aka ƙulla tsakanin gwamnati da Abzinawa. Jaridar ta ce:

„A tattaunawar farko kai tsaye tsakanin gwamnatin Mali da ƙungiyoyi biyu na 'yan tawayen Abzinawa da suka mamaye arewacin ƙasar, Abzinawa sun amince da zaman ƙasar a matsayin tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Tattaunawar da aka yi a birnin Ouagadougou na ƙasar Burkina Faso, ya samu halarcin ƙungiyar MNLA da wakilan ƙungiyar Ansar Dine. Kungiyoyin biyu da gwamnatin Mali sun amince da shirin tsagaita wuta a wani mataki na samar da kyakkyawan yanayin ci gaba da tattaunawa. Jaridar ta ce bisa ga dukkan alamu kungiyar MNLA ta yi watsi da bukatar kafa ƙasar Abzinawa, maimakon haka yanzu take magana yankin Azawad mai ƙwarya-ƙwaryar 'yancin cin gashin kai. Sai dai har yanzu ba a tantance batun shari‘a ba. Ko da yake Ansar Dine ta yi watsi da bukatar kafa shari'a a ilahirin kasar ta Mali, amma ta ɗage da ci gaba da amfani da dokokin Musulunci a yankunan dake ƙarƙashin ikonta.“

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland wadda a labarinta a kan zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokokin ƙasar Ghana ta fara da cewa zaɓe a wata ƙasar Afirka mai samun bunƙasar tattalin arziki, sannan ta ci gaba kamar haka.

Präsidentschaftswahl Ghana 2012
Hoto: DW/Usman Shehu Usman

„A zaɓen na wannan karon 'yan kasar Ghana za su zaɓi mutumin da suka amince da shi ne wanda zai yi amfani da kuɗaɗen mai a hanyoyi mafi dacewa don yaƙi da talauci. Jaridar ta ce godiya ta tabbata da arzikin man fetir, a bara Ghana ta samu bunƙasar kashi 14 cikin 100 wanda ke zaman mafi yawa a duniya. Sai dai a lokaci ɗaya kashi ɗaya cikin uku na al'umar kasar su kimanin miliyan 20 na rayuwa hannu baka hannu ƙwarya, sannan daidai wannan adadi ba su iya rubutu da karatu ba. A shekarun baya bayan nan Accra babban birnin ƙasar ya zama wani dandalin gine gine inda kamfanonin kasashen duniya ke gina manyan kantuna da gidaje. Sai dai wannan ci gaba bai kai yankin arewacin kasar ba, inda kawo yanzu mazauna wannan yanki ba su fara ɗanɗana arzikin man fetir ɗin ba. Hasali ma wani rahoton bankin duniya cewa yayi daga 1995 zuwa 2006, 'yan arewacinn Ghana musamman matasa kimanin miliyan 2.5 suka yi ƙaura zuwa kudancin kasar don ƙaurace wa talauci da fatara. Saboda haka nauyin dake kan sabon shugaban kasa zai zama bunƙasa aikin noma dake zama babbar sana'ar akasarin 'yan arewacin kasar da tallafa wa ƙananan kamfanoni don ƙirƙiro aikin yi.“

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung tsokaci ta yi kan halin da ake ciki a Kongo. Jaridar ta ce:

Ostkongo Goma Rebellen verlassen Goma
Hoto: Simone Schlindwein

„Sojojin gwamnati sun koma birnin Goma, amma ‚yan tawayen M23 sun yi barazanar kai sabon farmaki idan shugaba Joseph Kabila ya ki zaman teburin shawarwari da su. Sannu a hankali rayuwa ta koma yadda akan saba a birnin Goma, kuma yanzu haka bayan ‚yan sanda, su ma sojojin Kongo sun koma birnin dake gabashin kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, shi ma gwamnan lardin Kivu ta Arewa ya koma fadarsa bayan ya tsere daga ‚yan tawaye. Sai dai ana shakku ko zaman lafiyar zai dore.“

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh