Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A Najeriya masana sun nunar da cewa hanya mafi sauki ta dakile son tafiya ci-rani zuwa Turai da matasan kasar ke yi, ita ce karfafa musu guiwar kama kananan sana’o’i musamman na hannu.
Wasu jandarmomi a Agadez Jamhuriyar Nijar dubunsu ta cika bayan da aka kamasu da karbar cin hanci a hannun bakin haure, abin da ke nuna irin kalubale da su ke fiskanta a hanyar zuwa Turai bayan ratsa Libiya ko Aljeriya.
Ko da shike a yanzu kasashen Turai sun tashi haikan don magance matsalar bakin haure, duk haka masu safarar mutanen kan bi wasu sabbin hanyoyi na daban a tsakiyar sahara. Akwai matukar bukatar masu sana'ar yin somogan mutane su sauya.
Libiya dai ta zama wata babbar hanyar da dubban bakin haure ke bi don tsallakawa zuwa Turai ta tekun Bahrum
Da yawa daga cikin matan Afirka da ke tilastawa yin karuwanci a Turai 'yan Najeriya ne.
Farautar matasa da ke kan hanyarsu ta zuwa Turai, ana rudinsu cewar za a shige da su ta Sahara.
Tafiyar hawainiya wajen cika alkawuran da aka yi wa matasa masu safarar bakin haure na samar musu da aikin yi na halan.
Ghana na a jerin kasashen Afirka da ke a sahun gaba wajen fitar matasansu zuwa kasashen waje musamman Turai da Amirka ko Saudiyya da kwadayin samun ingantacciyar rayuwa.
Yayinda suke fafitikar samun izinin mafakar siyasa a Jamus, 'yan gudun hijirar Gambiya na lura da yanayin siyasar kasarsu bayan shekaru 22 da mulkin Yahya Jammeh.
Ali Koury da ya rasa dansa a cikin 'matasan Senegal da ke kaura zuwa Turai, ya kafa wata kungiya ta wadanda suka bace.
Dame Sylla da ya samu horo daga kungiyar ASPAIL ya ce yana da kyakkyawar makoma a Senegal.
Daruruwan 'yan Afirka na mutuwa a Tekun Bahar Rum a kokarin shiga nahiyar Turai.
'yan ci-rani masu neman zuwa Turai sun dauki Jamhuriyar Nijar a matsayin hanya wucewa domin isa inda suka saka a gaba.