Hana fadin albarkacin baki a Najeriya | Labarai | DW | 12.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hana fadin albarkacin baki a Najeriya

An dai karbe takardar izinin daukar labarai a fadar shugaban kasa da aka bai wa Ubale Musa wakilin DW , biyo bayan wata tambaya ga shugaban Chadi da 'yan Najeriya ke neman amsarta.

DW-Korrespondendent Ubale Musa

Ubale Musa wakilin DW Hausa

Cikin sakon da ya aiki wa gwamnatin Najeriya ta hanyar ofishin mai bada shawara ta musamman ga shugaban Najeriyar Mista Reuben Abati, amadadin shugaban gidan rediyon DW Peter Limburg, shugaban sashin harkokin sadarwa kuma jami'in da ke lura da harkokin yada labarai Christoph Jumpelt , ya bayyana bakin cikinsa da yadda aka fitar da Ubale Musa daga cikin jerin 'yan jarida da ke halartar taron manema labarai a fadar shugaban kasa.

Wannan dai na zuwa ne bayan tambayar shugaban kasar Chadi Idris Derby kan dalilan shigar dakarun sojan haya daga Afrika ta Kudu cikin sojan kawancen yaki da Boko Haram abin da bai sabawa aikin jarida ba.

Da ya ke bayyana Ubale Musa a matsayin haziki kuma kwararren dan jarida da ke aiki bisa sharuda, mista Jumpelt ya ce wannan ba shi ne karon farko ba da ake wa ma'aikatan DW shinge a lokacin gudanar da ayyukansu, musamman a baya-bayan nan a lokacin zaben kasar na 2015.

Ya ce ba karamin take hakki ba ne a tilasta ficewar dan jarida bisa umarnin mai bada shawara a harkokin tsaro irin wannan, dan haka sai ya bukaci cikin gaggawa da a mai da wa Ubale Musa kati na aiki a wannan fada ta shugaban kasa kamar yadda jami'an gwamnatin Najeriyar suka yi alkawari.

Tashar dai ta DW na aikin ta ne na jarida a Najeriya inda al'ummar wannan kasa da dama ke cin moriya ayyukanta kuma ta ke fatan 'yan jarida za su samu cikakkiyar damar gudanar da aikinsu ba tare da tsangwama ba.

Ubale Musa dai ya kasance yana aiki da DW tun daga shekarar 1998 kuma shi ne wakilinta a fadar shugaban kasar Najeriya da ke Abuja.