Hamburg: An maida binciken hari ga tarayya | Labarai | DW | 31.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hamburg: An maida binciken hari ga tarayya

Masu gabatar da kara na tarayyar Jamus sun karbi ragamar gudanar da binciken mummunan hari da wuka da aka kai a Hamburg

Babbabn lauya mai gabatar da kara na Jamjus ya sanar da karbar ragamar gudanar da binciken harin da aka kai da wuka a birnin Hamburg a ranar juma'ar da wuce, inda wani matashi dan gudun hijira mai 26 da haihuwa ya kashe mutum daya ya kuma jiwa wasu mutanen shida raunuka.

Kakakin mai gabatar da karar Frauke Koehler ta ce an karbe ragamar binciken ne saboda muhimmancin karar sannan ana so a bi diddigin makasudin harin.

Mutumin da ake zargi da kai harin wani mai tsattsauran akida dan kungiyar IS sananne ne ga hukumomin tsaron Jamus. Sai dai an yi imanin yana da matsaloli na tabin hankali.